ABNA24 : Ana dai kallon wannan a matsayin wani sabon babi tsakanin kasashen biyu, bayan tsamin dangantaka da kisan da akayi wa dan jaridan a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na birnin Santambul ya haifar.
Dama dai Saudiyya da Turkiyya suna da sabanin kan batutuwa da dama, musamman goyan bayan da Turkiyya ta baiwa Qatar lokacin da Saudiyyar da kawayenta suka yanke alaka da Qatar.
A bnagaren Saudiyya kuwa akwai makarantun Turkiyya da dama da aka rufe, sannan kuma Saudiyya ta kauracewa wasu kaya na Turkiyya duk da cewa ba a hukumance ne ba.
Ana dai ganin bangarorin biyu zasuyi amfani da wannan damar ta ziyarar da Mevlut Cavusoglu, zai kai Saudiyya domin warware sabanin dake a tsakaninsu.
A baya bayan nan dai an ga ministan harkokin wajen Turkiyya, na nun adamuwarsa kan hare haren da ‘yan Houtsis na Yemen, ke kai wa kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya.
342/